Universal Declaration of Human Rights - Hausa (2) This plain text version prepared by the "UDHR in XML" project, http://efele.net/udhr. ----- Kalamin duniya gaba ɗaya na kare hakkin ɗan Adam Gabatarwa Ganin cewa aminincewa da muhimmancin mutuncin da ya rataya ga dukkan mambobin iyali na bil Adama da kuma ƴancinsu da yake daidai kuma ya halatta garesu ya zama shine ginshikin ƴanci, da shari’a da kuma zaman lafiya a cikin duniya, Ganin cewa ƙin amincewa da rena hakkin ɗan Adam sune suka haddasa aikin assha da tada ƙayar bayan lamarin bil Adama da kuma cewa shigowar sabon al’amari na duniya inda mutane za su samu ƴancin magana da tunani, su rabu da tsoro da bala’i, shine aka bayyana kamar babban kishin zucin ɗan Adam, Ganin cewa ya muhimminta mulki mai kare ƴanci ya kare hakkin ɗan Adam saboda kada mutum ya matsu, a mafita ta ƙoli, har ya kai ga tada ƙayar baya game da girman kai da zalunci, Ganin cewa ya muhimminta a bada ƙwarin gwiwa ga ci gaban dangantaka tsakanin ƙasashe, Ganin cewa cikin usula, al’ummomin ƙasashen ɗinkin duniya sun bayyana hal wa yau imaninsu ga cikakkun tsare-tsaren shari’ar ɗan Adam, cikin mutunci da darajar mutum, cikin daidaicin hakkin maza da mata, kuma suka bayyana tashi tsaye a kai don fifita ci gaban al’umma da kafa datattun halayen rayuwa cikin wadataccen ƴanci, Ganin cewa ƙasashe mambobi sun ɗauki nauyin tabbatar da, cikin hulɗa tare da majalisar ɗinkin duniya, cikakkar biyayya cikin duk faɗin duniya ga hakkin ɗan Adam da ƴanci mai muhimmanci, Ganin cewa samun manufa ɗaya na waɗannan hakkoki da ƴanci shi ne mahi muhimmanci don cika wannan nauyin, Babban taro Yana bayyana wannan kalamin duniya gaba ɗaya na kare hakkin ɗan Adam tamkar aƙidar da duk al’ummomi da duk ƙasashe ya kamata su cimma domin dukkan mutane da dukkan ƙungiyoyin al’umma, waɗanda suke da wannan kalamin a cikin tunanisu na ko da yaushe, su dage, da koyarwa da bada ilimi da horo, don tabbatar da biyayya ga waɗannan hakkoki da ƴanci a kuma tabbartar da, game da matakan ci gaba na tsarin cikin ƙasa da ƙasashe, cikakkar yarda da cikakken aiki na duniya baki ɗaya, ko ya kasance daga cikin jama’ar ƙasashe mambobi su da kansu ko kuma ya kasance cikin jama’ar yankunan da aka sa ƙarƙashin ikonsu. Ayar doka ta ɗaya Ana haihuwar duk mutane da ƴancinsu da kuma daidaici tsakaninsu dangane da mutunci da hakki. Suna da hankali da kima da natsuwa kuma ya kamata su haɗa kansu. Ayar doka ta 2 Kowa yana iya buga gaba ga dukkan hakki da ƴanci da aka bayyana a cikin wannan kalamin duniya, babu duk wani bambanci, musamman na ƙabila, da launin fata, da jinsi, da yare, da addini, da ra’ayin siyasa ko duk wani irin ra’ayi, da asalin ƙasa ko na jama’a, da na arziki, da haifuwa ko dukkan wani iri hali. Bugu da ƙari, ba za a yi bambanci ko ɗaya ba wanda ta kafu bisa matsayin siyasa, na shari’a ko na ƙasashe daga ƙasa ko yankin da mutum ya fito, ƙasar ko yankin ya zamana mai ƴanci kanshi ne, na ƙarƙashi wani ne, mai rishin ƴanci kai ko wanda aka tauye ma wani ƴanci kai. Ayar doka ta 3 Kowane mutum ya na da ƴancin rayuwa, da ƴancin walawa da kuma kwanciyar kankalin kanshi Ayar doka ta 4 Ba wanda za a ɗauka da sunan bauta ko aikin badala; an hana kowaɗane irin siffofin bauta ko fataucin bayu Ayar doka ta 5 Ba wanda za a azabatar, ko muzguna ko dukan rishin imani, ko mai taɓarɓare jiki. Ayar doka ta 6 kowa ya na da ƴancin a karɓe shi a matsayinshi na ɗan Adam a ko’ina Ayar doka ta 7 Dukan mutane suna da matsayi ɗaya gaban doka kuma suna da ƴancin samun kariya iri ɗaya ta doka ba tare da bambanci ba. Kowa na da ƴancin samun kariya iri ɗaya daga duk wani nuna bambanci wanda za ta karya wannan kalamin kuma daga duk taƙula dangane da wannan bambancin. Ayar doka ta 8 Kowane mutum ya na da ƴancin ɗaukaka ƙara gaban ƙwararrin hukumomin ƙasa game da ayyuka masu karya muhimman hakkokinshi waɗanda tsarin mulki da doka suka amince da su. Ayar doka ta 9 Ba wanda za a kama ba tare da hujja ba, ɗan kaso ko ɗan gudun hijira. Ayar doka ta 10 Kowane mutum yana da ƴanci, a cikakken daidaici, da kotu mai ƴancin kanta da rishin nuna son rai ta saurari kukanshi yadda ya kamata kuma a gaban jama’a, wanda za ta yanke hukunci, ko hakkinshi da abubuwa da suka wajabta gare shi, ko da gaskiyar tuhumar da aka yi mishi. Ayar doka ta 11 Duk mutumen da aka tuhuma da wani laifi yana nan zaman maras laihi har sai in halin laifinshi ya bayyana lokacin gudanar da shari’a gaban jama’a wurin da ya samu dukkan datattun abubuwan da suka tabbata ga kare shi. Ba wanda za a sa kaso saboda aikata ayyuka ko mantuwa, waɗanda a lokacin da ya akaita su, ba su kasance laifi ba a cikin tsarin shari’a na ƙasa ko na ƙasashen duniya. Haka kuma, ba za a yi mishi hukunci mai ƙarfi ba fiye da wanda ya kamata a yi mishi lokacin da ya aikata laihin. Ayar doka ta 12 Ba wanda za a yi ma shiga-shugula na ba dalili a cikin rayuwarshi, iyalinshi, gidanshi ko alaƙarshi, ko taɓa mutuncinshi ko sunanshi. Kowane mutum na da ƴanci doka ta kare shi game da dukkan shiga- shugula ko wannan taɓa hakki. Ayar doka ta 13 Kowane mutum yana da ƴancin yawo yadda ya buƙata kuma ya zaɓi mazauninshi a cikin ƙasa. Kowane mutum yana da ƴanci barin kowace ƙasa, har ma da tashi, kuma ya dawo cikinta Ayar doka ta 14 Game da tsanani muzgunawa, kowane mutum yana da ƴancin neman mafaka da kuma samun mafaka a cikin wasu ƙasashe. Ba za a yi zancen wannan ƴanci ba cikin zargin da aka tabbatar game da wani kisan kai na doka gama-gari ko wasu tashe-tashen hankulla da suka saɓa ma manufofi da aƙidar majalisar ɗinkin duniya. Ayar doka ta 15 Kowane mutum yana da ƴancin samun takardar shaidar cika ɗan ƙasa Ba wanda za a hana ma takardarshi ta shaidar cika ɗan ƙasa ba da wata hujja ba, ko a hana shi ƴancin canza takardarshi ta shaida. Ayar doka ta 16 Daga an kai shekarar aure (balaga), namiji da mace, kada a tauye wani abu dangane da ƙabila, shaidar cika ɗan ƙasa ko addini, suna da ƴancin su yi aure kuma su kafa iyali, ƴancinsu ya daidaita bisa abun da ya shafi aure, cikin zaman aure da lokacin rabuwarshi. Kada a tsaida zancen aure ba tare da cikakkar yardar ma’auratan ba. Iyali shine ginshiƙin al’umma mahi muhummanci kuma yana da ƴancin samun kariya daga al’umma da ƙasa. Ayar doka ta 17 Mutum ya zamana shi kaɗai ko tare da jama’a, yana da ƴancin samun mazaumi. Ba wanda za a raba da mazauninshi ba tare da wata hujja ba. Ayar doka ta 18 Kowane mutum yana da ƴancin yin nazari, da sanin ciwon kai da addini; wannan hakki na bada ƴancin canza addini ko na tabbaci da kuma ƴancin nuna addininshi ko tabbacinshi, shi kaɗai ko tare da jama’a, cikin bainar jama’a ko a keɓance, ta hanyar koyarwa, tabi’o’i, bautawa wani abu da aikata ibadodi. Ayar doka ta 19 Kowane mutum yana da ƴancin ra’ayi da na magantawa, wannan ne ke ba shi ƴancin rishin damuwa game da ra’ayoyinshi da na neman labaru da ra’ayi, na samunsu da kuma na yaɗasu, ba tare da kula da iyakoki ba, ta kowace hanyar magantawa. Ayar doka ta 20 Kowane mutum yana da ƴancin yin shawara da ƴancin kafa ƙungiya cikin kwanciyar hankali. Ba wanda za a tilasta ma shiga wata ƙungiya. Ayar doka ta 21 Kowane mutum yana da ƴancin halarta wajen gabartar da ayyukan jama’a na ƙasarshi, kai tsaye, ko kuma ta hanyar wani wakili da ya zaɓa. Kowane mutum yana da ƴancin samun aikin gwamnati na ƙasarshi a cikin halin daidaici. Niyyar jama’a ita ce ginshiƙin ikon hukumominta; ya kamata a bayyana wannan niyya ta hanyar zaɓuɓɓuka na gaskiya waɗanda za a yi su lokaci zuwa lokaci, ga zaɓen da ya shafi kowa da kowa da zaɓe cikin sirri ko ga ɗaukan matakin da zai tabbatar da ƴancin zaɓe Ayar doka ta 22 Duk mutum, a matsayinshi na mamba na ƙungiya, yana da ƴancin samun kwanciyar hankalin jama’a, an girka ta ne don samun biyan buƙatar ƴancin tattalin arziki, na jama’a da al’adu masu muhimmanci ga mutuncinshi da ci gaban kanshi, a dalilin ƙoƙarin ƙasa da na hulɗar ƙasashe, dangane da tsari da kuma ma’adanan kowace ƙasa. Ayar doka ta 23 Kowane mutum yana da ƴancin samun aiki, da ƴancin zaɓen aikinshi, dangane da gamsassun halayen gaskiya na aiki da kuma na kariya game da rishin aiki. Kowa na da ƴanci, ba tare da nuna bambanci ba, na samun albashin da ya dace da aikinshi. Duk wanda ya yi aiki yana da ƴancin samun gamsashen albashi na gaskiya wanda zai tabbatar mishi, shi da iyalinshi ingantattar rayuwa daidai da mutuncin ɗan Adam, da son samu, har ma da hanyoyin kariyar jama’a. Kowane mutum yana da ƴancin kafa ƙungiya tare da wasu mutune ko kuma goyon bayan wasu ƙungiyoyin da za su kare amfaninshi. Ayar doka ta 24 Kowane mutum yana da ƴancin samun hutu da shaƙatawa musamman ma dangane da daidata tsawon lokacin aiki da kuma hutun lokaci zuwa lokaci. Ayar doka ta 25 Kowane mutum yana da ƴancin samun wadataccen matsayin rayuwa don tabbatar da lafiyarshi, jin-daɗinshi da na iyalinshi, musamman ma na abinci, sutura, mazauni, maganin likita da sauran buƙatocin da suka dace, yana da ƴancin samun kwanciyar hankali a lokacin zaman rishin aiki, rishin lafiya, gazawa, takaba, tsufa ko lokacin da ya shiga cikin wasu halaye na rishin abinci dangane da wasu abubuwa da suka faru ba tare da son shi ba. Daga ɗaukar ciki har zuwa haifuwa da renon yaro suna da ƴancin samun taimako da kulawa na musamman. Dukkan yara, su zamana waɗanda aka haifa da aure ko babu aure, suna da ƴacin samun kariyar jama’a. Ayar doka ta 26 Kowa na da ƴancin samun horo da ilimi. Ya kamata ilimi da horo ya zama na kyauta, ko da wanda ya shafi ƙananan makarantu ne. Koyarwa ta ƙananan makarantu ta zama tilas. Ya kamata a yaɗa koyarwa ta fusa’a da koyon sana’a; ya kamata kowa ya samu shiga makarantun koyon ilimi mai zurfi dangance da cancantarshi ba tare da bambanci ba. Ya kamata horo ya danganta da cikakken jin daɗin rayuwar mutum da ƙarfafa ladabi ga hakkin ɗan Adam da muhimman ƴanci. Ya kamata ya fifita fahimta, yafiya, da amintaka tsakanin dukkan ƙasashe da dukkan gungunnan ƙabilu ko na addini, haka kuma ci gaban ayyukan majalisar ɗikin duniya na tabbatar da zaman lafiya Uwaye sune a farko, suke da ƴancin zaɓen irin horon da za a baiwa ƴaƴansu. Ayar doka ta 27 Kowane mutum yana da ƴancin halartar al’adar rayuwar al’umma, yayi amfani da fusa’arsu kuma ya sa hannu ga ci- gaban ilimin kimiyya da abubuwa na alhairi da ke cikinsu Kowa yana da hakkin kariyar abubuwan amfani na jama’a da waɗanda aka samu sakamakon aikin kimiyya, na adabi ko na aikin zane-zanen da ya wallafa. Ayar doka ta 28 Kowane mutun yana da hakki, bisa tsarin jama’a da tsarin ƙasashe, umurni ya gudana kamar hakkoki da ƴancin da aka gabatar a cikin wannan kalami su samu aikinsu ya ci da kyau. Ayar doka ta 29 Mutum yana da abubuwan da suka wajaba gareshi game da al’umma wadda a cikin ta yake da damar samun ƴancin cikakken ci gaban kanshi. A cikin amfani da hakkinshi da kuma cin moriyar ƴancinshi, kowane mutum bai da ikon ya zarce ga dokkokin da aka shimfiɗa masu tabbatar da amincewa da yin ladabi ga hakki da ƴancin ɗan uwanshi kuma a ƙarshe don gamsar da buƙatocin ɗa’a, da tsarin jama’a da kuma jin ɗaɗi na galibi cikin al’ummar da aka kafa bisa tafarkin demokaraɗiya. Waɗannan hakkokin da ƴancin ba za su samu shiga ba, sam sam, matuƙar sun saɓa ma gurori da sharuɗɗan majalisar ɗinkin duniya. Ayar doka ta 30 Babu wani mataki na wannan kalamin da za a fasara shi tamkar ya shafi, ga wata ƙasa, wata ƙungiya ko wani mutum, wani ƴancin na dabam da zai ba da damar yin wani aiki ko ɗaukan wani mataki mai niyyar lalata hakkoki da ƴancin da aka bayyana.